Ishaya 10:9-14
9
‘Kalno bai kasance kamar Karkemish ba? Hamat bai zama kamar Arfad Samariya kuma kamar Damaskus ba?
10
Yadda hannuna ya ƙwace mulkokin gumaka, mulkokin da siffofinsu suka fi na Urushalima da Samariya,
11
ba zan yi da Urushalima da siffofinta yadda na yi da Samariya da gumakanta ba?’ ”
12
Sa’ad da Ubangiji ya gama dukan aikinsa gāba da Dutsen Sihiyona da Urushalima, zai ce, “Zan hukunta sarkin Assuriya saboda fariya na gangancin zuciyarsa da kuma kallon reni na idanunsa.
13
Gama ya ce, “ ‘Ta wurin ƙarfin hannuna ne na aikata wannan, da kuma ta wurin hikimata, gama ina da fahimi. Na kau da iyakokin ƙasashe, na washe dukiyarsu; a matsayina na mai iko, na mamaye sarakunansu.
14
Kamar yadda mutum yakan miƙa hannu cikin sheƙar tsuntsu haka hannuna ya je ya washe dukiyar al’ummai; kamar yadda mutane sukan tattara ƙwai, haka na tattara dukan ƙasashe; ba tsuntsun da ya kakkaɓe fikafiki, ko yă buɗe baki don yă yi kuka.’ ”
Settings