Ishaya 10:5-11
5
“Kaiton Assuriya, sandar fushina, a hannun da kulkin fushina yake!
6
Na aike shi gāba da al’umma marar sanin Allah, na tura shi gāba da mutanen da suka ba ni fushi, don yă kwashe ganima yă kuma yi wason ganima, yă tattake su kamar laka a tituna.
7
Amma ba abin da ya yi niyya ke nan ba, ba abin da yake da shi a zuciya ba; manufarsa shi ne yă hallaka, yă kuma kawo ƙarshen al’ummai da yawa.
8
Ya ce, ‘Dukan shugabannin yaƙina ba sarakuna ba ne?’
9
‘Kalno bai kasance kamar Karkemish ba? Hamat bai zama kamar Arfad Samariya kuma kamar Damaskus ba?
10
Yadda hannuna ya ƙwace mulkokin gumaka, mulkokin da siffofinsu suka fi na Urushalima da Samariya,
11
ba zan yi da Urushalima da siffofinta yadda na yi da Samariya da gumakanta ba?’ ”
Settings