Ishaya 10:28-34
28
Sun shiga Ayiyat; sun bi ta Migron; sun adana tanade-tanade a Mikmash.
29
Suka ƙetare ta hanya, suka kuma ce, “Za mu kwana a Geba.” Rama ta firgita; Gibeya ta Shawulu ta gudu.
30
Ki yi ihu, ya Diyar Gallim! Ki saurara, ya Layisha! Kayya, Anatot abin tausayi!
31
Madmena tana gudu; mutanen Gebim sun ɓuya.
32
A wannan rana za su dakata a Nob; za su jijjiga ƙarfinsu a dutsen Diyar Sihiyona, a tudun Urushalima.
33
Duba, Ubangiji Maɗaukaki, zai ragargaza rassa da iko mai girma. Za a sassare itatuwa masu ganyaye, za a yanke dogayen itatuwa har ƙasa.
34
Zai sassare itatuwan jeji da gatari har ƙasa; Lebanon zai fāɗi a gaban Mai Iko.
Settings