Ishaya 11:1-5
1
Toho zai fito daga kututturen Yesse; daga saiwarsa Reshe zai ba da ’ya’ya.
2
Ruhun Ubangiji zai kasance a kansa, Ruhun hikima da na fahimta, Ruhun shawara da na iko, Ruhun sani da na tsoron Ubangiji,
3
zai kuwa ji daɗin tsoron Ubangiji. Ba zai yi hukunci ta wurin abin da ya gani da idanunsa ba, ba zai kuwa yanke shawara ta wurin abin da ya ji da kunnuwansa ba;
4
amma da adalci zai yi wa masu bukata shari’a, da gaskiya zai yanke shawarwari saboda matalautan duniya. Kamar sanda zai bugi duniya da maganar bakinsa; da numfashin leɓunansa zai yanke mugaye.
5
Adalci ne zai zama abin ɗamararsa aminci kuma igiyar da zai ɗaura kewaye da gindinsa.
Settings