Hosiya 4:12-19
12
Sun nemi shawarar gunkin da aka yi da itace suka kuwa sami amsa daga sanda. Halin karuwanci yakan ɓad da su; sun yi rashin aminci ga Allahnsu.
13
Suna miƙa hadaya a kan ƙwanƙolin duwatsu suna kuma ƙone hadayu a kan tuddai, a ƙarƙashin itatuwa oak, aduruku da katambiri, inda inuwa take da daɗi. Saboda haka ’ya’yanku mata suka juya wa karuwanci surukanku mata kuma suka shiga yin zina.
14
“Ba zan hukunta ’ya’yanku mata sa’ad da suka juya ga yin karuwanci ba, balle surukanku mata, sa’ad da suka yi zina, gama mazan da kansu suna ma’amala da karuwai suna kuma miƙa hadaya tare da karuwai na masujada, mutane marasa ganewa za su lalace!
15
“Ko da yake kun yi zina, ya Isra’ila, kada Yahuda ya yi laifi. “Kada ku tafi Gilgal; kada ku haura zuwa Bet-Awen. Kuma kada ku rantse cewa, ‘Muddin Ubangiji yana a raye!’
16
Isra’ilawa masu taurinkai ne, kamar karsana mai taurinkai. Yaya Ubangiji zai iya kiwonsu kamar tumaki a makiyaya mai ɗanyar ciyawa?
17
Efraim ya haɗa kai da gumaka; ku ƙyale shi kurum!
18
Ko ma sa’ad da abin shansu ya ƙare, sai suka ci gaba da karuwancinsu; masu mulkinsu suna ƙaunar abin kunya.
19
Guguwa za tă share su, hadayunsu kuma za su jawo musu abin kunya.
Settings