Hosiya 1:1-2
1
Maganar Ubangiji da ta zo wa Hosiya ɗan Beyeri a zamanin mulkin Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, sarakunan Yahuda, da zamanin mulkin Yerobowam ɗan Yowash sarkin Isra’ila.
2
Sa’ad da Ubangiji ya fara magana ta wurin Hosiya, Ubangiji ya ce masa, “Ka tafi, ka auro wa kanka mazinaciya da ’ya’yan da aka haifa ta hanyar rashin aminci, domin ƙasar tana da laifin mummunan zina ta wurin rabuwa da Ubangiji.”
Settings