Skip to content
Ibraniyawa 13:10-17

Ibraniyawa 13:10-17

10
Muna da bagade inda firistocin da suka yi hidima a tabanakul ba su da izini su ci.
11
Babban firist yakan ɗauki jinin dabbobi yă shiga cikin Wuri Mafi Tsarki a matsayin hadaya ta zunubi, amma jikunan dabbobin akan ƙone su a bayan sansani.
12
Haka ma Yesu ya sha wahala a bayan gari don yă tsarkake mutane ta wurin jininsa.
13
Saboda haka, sai mu fita mu je wajensa a bayan sansani, muna ɗaukar kunyar da ya sha.
14
Gama a nan ba mu da dawwammamen birni, sai dai muna zuba ido a kan birnin nan mai zuwa.
15
Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah, yabon leɓuna da yake shaidar sunansa.
16
Kada kuma ku manta yin aikin nagari da kuma taimakon waɗansu, gama da irin waɗannan hadayu ne Allah yake jin daɗi.
17
Ku yi wa shugabanninku biyayya ku kuma miƙa kanku ga ikonsu. Suna lura da ku kuma za su ba da lissafi a gaban Allah. Saboda haka kada ku sa su yi fushi saboda aikinsu, ku sa su yi farin ciki. In ba haka ba za su iya taimakonku ba ko kaɗan.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options