Habakkuk 1:8-17
8
Dawakansu sun fi damisoshi sauri, sun fi kyarketan yamma zafin rai. Mahayansu suna zuwa a guje; mahayansu daga nesa suka fito. Suna firiya kamar ungulu mai sauka da gaggawa don yă ci mushe;
9
duk sukan zo da nufin tā-da-na-zaune-tsaye. Ana jin tsoronsu tun ma kafin su iso suna tattara bayi kamar yashi.
10
Sukan yi wa sarakuna ba’a su kuma rena masu mulki. Sukan yi wa dukan birane masu mafaka dariya; sukan tara ƙasa su hau, su cinye abokan gābansu da yaƙi.
11
Sa’an nan su wuce da sauri kamar iska, mutane ne masu laifi, waɗanda ƙarfinsu shi ne allahnsu.”
12
Ya Ubangiji, ba tun fil azal kake ba? Ya Allahna, Mai Tsarkina, ba za mu mutu ba. Ya Ubangiji ka sanya su su tabbatar da hukunci; Ya Dutse, ka naɗa su don su yi hukunci.
13
Idanunka masu tsarki ne da suka fi gaban duban mugunta; ba ka amince da abin da ke ba daidai ba. To, don me ka ƙyale munafukai suna cin karensu ba babbaka? Me ya sa kake shiru sa’ad da mugaye suke haɗiye adalai da suka fi su adalci?
14
Ka mai da maza kamar kifin teku, kamar halittun tekun da ba su da shugaba.
15
Mugu abokin gāba yakan kama su duka da ƙugiya, yă jawo su waje da abin kamun kifinsa, yă tattara su cikin ragarsa, ta haka yakan yi murna da farin ciki.
16
Saboda haka yakan yi hadaya wa abin kamun kifinsa yă kuma ƙona turare wa ragarsa, domin ta wurin abin kamun kifinsa ne yake yin rayuwar jin daɗi yă kuma zaɓi irin abincin da yake so.
17
Zai ci gaba da juye abin kamun kifinsu ke nan, suna hallaka al’ummai ba tausayi?
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings