Skip to content
Habakkuk 1:5

Habakkuk 1:5

Ana nuna aya 5 tare da mahallin da ke kewaye.
2
Har yaushe, ya Ubangiji, zan yi kukan neman taimako, amma ka ƙi ji? Ina kuka a gare ka saboda zalunci amma ba ka ce ufam ba.
3
Me ya sa ka bari ina ta kallon rashin gaskiya? Me ya sa kake barin abin da ba daidai ba? Hallaka da tashin hankali suna a gabana; ga rashin jituwa da faɗa ko’ina.
4
Saboda haka ba a bin doka, shari’a kuma ba ta aiki. Mugaye sun kewaye masu adalci don a hana gaskiya tă yi aiki.
5
“Ka dubi al’ummai, ka gani, ka sha mamaki. Ga shi zan yi wani abu a kwanakinka, wanda ko ma an faɗa maka ba za ka gaskata ba.
6
Zan tā da Babiloniyawa, waɗannan marasa hankali da kuma marasa tausayi; masu gajeren haƙuri, waɗanda suke ratsa ko’ina a duniya don su ƙwace wuraren zaman da ba nasu ba.
7
Suna da bantsoro da firgitarwa; dokoki da ƙa’idodinsu ne kawai suka sani.
8
Dawakansu sun fi damisoshi sauri, sun fi kyarketan yamma zafin rai. Mahayansu suna zuwa a guje; mahayansu daga nesa suka fito. Suna firiya kamar ungulu mai sauka da gaggawa don yă ci mushe;
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 90 chars

Options