Farawa 50:1-9
1
Yusuf kuwa ya fāɗa a kan mahaifinsa, ya yi kuka a kansa, ya kuma sumbace shi.
2
Sa’an nan Yusuf ya umarci masu maganin da suke yin masa hidima, su shafe mahaifinsa Isra’ila da maganin hana ruɓa. Saboda haka masu maganin suka shafe shi da maganin hana ruɓa.
3
Suka ɗauki kwana arba’in cif suna yin wannan, gama kwanakin da ake bukata ke nan don shafewa da maganin hana ruɓa. Masarawa kuwa suka yi makoki dominsa kwana saba’in.
4
Sa’ad da kwanakin makoki suka wuce, sai Yusuf ya ce wa iyalin gidan Fir’auna, “In na sami tagomashi a idanunku, ku yi magana da Fir’auna domina. Ku faɗa masa,
5
‘Mahaifina ya sa na yi rantsuwa, ya kuma ce, “Ina gab da mutuwa, ka binne ni a kabarin da na haƙa wa kaina a ƙasar Kan’ana.” Yanzu fa bari in haura in binne mahaifina, sa’an nan in dawo.’ ”
6
Fir’auna ya ce, “Haura ka binne mahaifinka, kamar yadda ya sa ka rantse za ka yi.”
7
Saboda haka Yusuf ya haura don yă binne mahaifinsa. Dukan hafsoshin Fir’auna suka yi masa rakiya tare da manyan mutanen gidan Fir’auna, da kuma dukan manyan mutanen Masar
8
da kuma dukan membobin gidan Yusuf, da ’yan’uwansa da kuma waɗanda suke na gidan mahaifinsa. Yara kaɗai da garkunansu da kuma shanunsu ne aka bari a Goshen.
9
Kekunan yaƙi da mahayan dawakai su ma suka haura tare da shi. Babbar ƙungiya jama’a ce ƙwarai.
Settings