Skip to content
Farawa 49:1-19

Farawa 49:1-19

1
Sai Yaƙub ya kira ’ya’yansa maza ya ce, “Ku tattaru don in faɗa muku abin da zai faru gare ku, a kwanaki masu zuwa.
2
“Ku tattaru, ku saurara, ’ya’yan Yaƙub maza; ku saurari mahaifinku, Isra’ila.
3
“Ruben, kai ne ɗan farina, ƙarfina, alamar farko ta ƙarfina, mafi matsayi, kuma mafi iko.
4
Mai tumbatsa kamar ruwa, amma ba za ka ƙara zama mai daraja ba, gama ka hau gadon mahaifinka ka hau kujerata, ka kuma ƙazantar da shi.
5
“Simeyon da Lawi ’yan’uwa ne, takubansu makamai ne na tā da hankali.
6
Ba zan shiga shawararsu ba, ba zan shiga taronsu ba, gama sun kashe maza cikin fushinsu cikin ganin dama suka kashe bijimai.
7
La’ananne ne fushinsu, mai tsanani ne ƙwarai, hasalarsu kuwa, muguwa ce ƙwarai! Zan warwatsa su cikin Yaƙub in kuma daidaita su cikin Isra’ila.
8
“Yahuda, ’yan’uwanka za su yabe ka; hannuwanka za su kasance a wuyan abokan gābanka, ’ya’yan mahaifinka maza za su rusuna maka.
9
Kai ɗan zaki ne, ya Yahuda, ka dawo daga farauta, ɗana. Kamar zaki, yakan kwanta a miƙe, kamar zakanya, wa yake da ƙarfin halin tashe shi?
10
Kursiyi ba zai tashi daga Yahuda ba, ba kuwa sandan mulki daga tsakani ƙafafunsa ba, sai ya zo ga wanda yake mai shi. Biyayyar al’umma kuwa tasa ce.
11
Zai daure jakinsa a kuringa, aholakinsa a rassa mafi kyau; zai wanke tufafinsa cikin ruwan inabi rigunansa cikin inabi ja wur kamar jini.
12
Idanunsa za su duhunce fiye da ruwan inabi, haƙorarsa farare kamar madara.
13
“Zebulun zai zauna a bakin teku, yă zama tasar jiragen ruwa; iyakarsa za tă nausa zuwa Sidon.
14
“Issakar doki mai ƙarfi, kwance tsakanin buhunan sirdi.
15
Sa’ad da ya ga yadda wurin hutunsa yana da kyau da kuma daɗin da ƙasarsa take, zan tanƙware kafaɗarsa ga nauyi yă miƙa kai ga aikin dole.
16
“Dan zai tanada adalci wa mutanensa kamar ɗaya cikin kabilan Isra’ila.
17
Dan zai zama maciji a gefen hanya, kububuwa a bakin hanya, da take saran ɗiɗɗigen doki domin mahayinsa yă fāɗi da baya.
18
“Ina zuba ido ga cetonka, ya Ubangiji.
19
“Masu fashi za su fāɗa wa Gad, amma zai runtume su.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options