Farawa 47:5-11
5
Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Mahaifinka da ’yan’uwanka sun zo maka,
6
ƙasar Masar kuma tana gabanka, ka zaunar da mahaifinka da ’yan’uwanka a sashe mafi kyau na ƙasar, bari su zauna a Goshen. Idan kuma ka ga waɗansu a cikinsu da suka fi dacewa, sai ka sa su lura mini da shanuna.”
7
Sa’an nan Yusuf ya shigar da Yaƙub mahaifinsa, ya gabatar da shi a gaban Fir’auna. Bayan Yaƙub ya albarkaci Fir’auna,
8
sai Fir’auna ya tambaye shi, “Shekarunka nawa da haihuwa?”
9
Yaƙub kuwa ya ce wa Fir’auna, “Shekarun hijirata, shekaru ɗari da talatin ne. Shekaruna kaɗan ne cike da wahala, ba za a kuwa daidaita su da shekarun hijirar kakannina ba.”
10
Sai Yaƙub ya albarkaci Fir’auna, ya yi masa bankwana, sa’an nan ya fita.
11
Ta haka Yusuf ya zaunar da mahaifinsa da ’yan’uwansa a Masar, ya ba su mallaka a sashe mafi kyau na ƙasar, a yankin nan na Rameses, kamar yadda Fir’auna ya umarta.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.