Farawa 41:37-57
37
Shirin ya yi wa Fir’auna da kuma dukan hafsoshinsa kyau.
38
Saboda haka Fir’auna ya tambaye su, “Za mu iya samun wani kamar wannan mutum, wannan wanda Ruhun Allah yake cikinsa?”
39
Sai Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Da yake Allah ya ba ka sanin dukan waɗannan, babu wani mai basira da kuma hikima kamar ka.
40
Za ka shugabanci fadata, kuma dukan mutanena za su zama a ƙarƙashinka. Da sarauta kaɗai zan fi ka girma.”
41
Saboda haka Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Ga shi na sa ka zama shugaban dukan ƙasar Masar.”
42
Sa’an nan Fir’auna ya zare zoben sarauta daga yatsarsa, ya sa shi a yatsan Yusuf. Ya sanya masa rigar lallausan lilin, ya kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa.
43
Ya sa shi ya hau keken yaƙi a matsayi mai binsa na biyu, mutane kuwa suka yi shela a gabansa suna cewa, “A ba da hanya!” Ta haka ya sa shi shugaba a kan dukan ƙasar Masar.
44
Sa’an nan Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Ni ne Fir’auna, amma in ba tare da umarninka ba, ba wanda zai ɗaga hannu ko ƙafa a cikin dukan Masar.”
45
Fir’auna ya ba wa Yusuf suna Zafenat-Faneya, ya kuma ba shi Asenat ’yar Fotifera firist na On, ta zama matarsa. Yusuf kuwa ya zaga dukan ƙasar Masar.
46
Yusuf yana zuwa shekara talatin sa’ad da ya shiga hidimar Fir’auna sarkin Masar. Yusuf kuwa ya fita daga gaban Fir’auna, ya zaga ko’ina a Masar.
47
A shekaru bakwai na yalwa, ƙasar ta ba da amfani mai yawa.
48
Yusuf ya tattara dukan abincin da aka samu a waɗannan shekaru bakwai na yalwa a Masar, ya kuma yi ajiyarsu a cikin birane. A kowane birni, ya sa abincin da aka nome a kewayensa.
49
Sai Yusuf ya tara hatsi da yawan gaske, kamar yashi a bakin teku, har sai da ya kāsa iya auna shi, gama ba a iya aunawa.
50
Kafin shekarun yunwa su zo, Asenat ’yar Fotifera, firist na On, ta haifa wa Yusuf ’ya’ya maza biyu.
51
Yusuf ya ba wa ɗansa na fari suna Manasse ya ce, “Gama Allah ya sa na mance dukan wahalata da dukan gidan mahaifina.”
52
Ya ba wa ɗansa na biyu suna Efraim ya ce, “Gama Allah ya wadata ni cikin wahalata.”
53
Shekaru bakwai na yalwa a Masar suka zo ga ƙarshe,
54
sai shekaru bakwai na yunwa suka soma shigowa, kamar yadda Yusuf ya faɗa. Aka yi yunwa ko’ina amma ban da ƙasar Masar. Don akwai abinci.
55
Sa’ad da dukan Masar ta fara jin yunwa, sai mutane suka yi wa Fir’auna kuka don abinci. Sai Fir’auna ya ce wa dukan Masarawa, “Ku tafi wurin Yusuf, ku kuma yi abin da ya faɗa muku.”
56
Sa’ad da yunwa ta bazu a dukan ƙasar, sai Yusuf ya buɗe gidajen ajiya, ya kuma sayar da hatsi ga Masarawa, gama yunwa ta yi tsanani a dukan Masar.
57
Dukan ƙasashe kuwa suka zo Masar don saya hatsi daga Yusuf, gama yunwa ta yi tsanani a dukan duniya.
Settings