Farawa 41:46-57
46
Yusuf yana zuwa shekara talatin sa’ad da ya shiga hidimar Fir’auna sarkin Masar. Yusuf kuwa ya fita daga gaban Fir’auna, ya zaga ko’ina a Masar.
47
A shekaru bakwai na yalwa, ƙasar ta ba da amfani mai yawa.
48
Yusuf ya tattara dukan abincin da aka samu a waɗannan shekaru bakwai na yalwa a Masar, ya kuma yi ajiyarsu a cikin birane. A kowane birni, ya sa abincin da aka nome a kewayensa.
49
Sai Yusuf ya tara hatsi da yawan gaske, kamar yashi a bakin teku, har sai da ya kāsa iya auna shi, gama ba a iya aunawa.
50
Kafin shekarun yunwa su zo, Asenat ’yar Fotifera, firist na On, ta haifa wa Yusuf ’ya’ya maza biyu.
51
Yusuf ya ba wa ɗansa na fari suna Manasse ya ce, “Gama Allah ya sa na mance dukan wahalata da dukan gidan mahaifina.”
52
Ya ba wa ɗansa na biyu suna Efraim ya ce, “Gama Allah ya wadata ni cikin wahalata.”
53
Shekaru bakwai na yalwa a Masar suka zo ga ƙarshe,
54
sai shekaru bakwai na yunwa suka soma shigowa, kamar yadda Yusuf ya faɗa. Aka yi yunwa ko’ina amma ban da ƙasar Masar. Don akwai abinci.
55
Sa’ad da dukan Masar ta fara jin yunwa, sai mutane suka yi wa Fir’auna kuka don abinci. Sai Fir’auna ya ce wa dukan Masarawa, “Ku tafi wurin Yusuf, ku kuma yi abin da ya faɗa muku.”
56
Sa’ad da yunwa ta bazu a dukan ƙasar, sai Yusuf ya buɗe gidajen ajiya, ya kuma sayar da hatsi ga Masarawa, gama yunwa ta yi tsanani a dukan Masar.
57
Dukan ƙasashe kuwa suka zo Masar don saya hatsi daga Yusuf, gama yunwa ta yi tsanani a dukan duniya.
Settings