Farawa 38:6-11
6
Sai Yahuda ya auro wa Er mata, ɗansa na fari, sunanta Tamar.
7
Amma Er, ɗan farin Yahuda mugu ne a fuskar Ubangiji, saboda haka Ubangiji ya kashe shi.
8
Sa’an nan Yahuda ya ce wa Onan, “Ka kwana da matar ɗan’uwanka ka cika wajibinka gare ta a matsayin ɗan’uwan miji, don ka samar wa ɗan’uwanka ’ya’ya.”
9
Amma Onan ya san cewa ’ya’yan ba za su zama nasa ba; saboda haka a duk sa’ad da ya kwana da matar ɗan’uwansa, sai yă zub da maniyyinsa a ƙasa don kada yă samar wa ɗan’uwansa ’ya’ya.
10
Abin nan da ya yi mugunta ce a gaban Ubangiji, saboda haka Ubangiji ya kashe shi, shi ma.
11
Sai Yahuda ya ce wa surukarsa Tamar, “Ki yi zama kamar gwauruwa a gidan mahaifinki sai ɗana Shela ya yi girma.” Gama ya yi tunani, “Shi ma zai mutu, kamar ’yan’uwansa.” Saboda haka Tamar ta je ta zauna a gidan mahaifinta.
Settings