Farawa 34:1-4
1
To, Dina, ’yar da Liyatu ta haifa wa Yaƙub, ta je ta ziyarci matan ƙasar.
2
Sa’ad da Shekem ɗan Hamor Bahiwiye mai mulkin wurin ya gan ta, sai ya kama ta, ya kwana da ita, ya ɓata ta.
3
Zuciyarsa kuwa ta damu da son Dina ’yar Yaƙub, ya kuwa ƙaunaci yarinyar, ya yi mata magana a hankali.
4
Sai Shekem ya ce wa mahaifinsa Hamor, “Ka auro mini wannan yarinya ta zama matata.”
Settings