Farawa 29:13-16
13
Nan da nan, da Laban ya sami labari game da Yaƙub, ɗan ’yar’uwarsa, ya gaggauta yă sadu da shi. Sai ya rungume shi ya sumbace shi, ya kuma kawo shi gidansa, a can kuwa Yaƙub ya faɗa masa dukan waɗannan abubuwa.
14
Sa’an nan Laban ya ce masa, “Kai nama da jinina ne.” Bayan Yaƙub ya zauna da shi na wata guda cif,
15
sai Laban ya ce masa, “Don kawai kai dangina ne na kusa, sai kawai ka yi mini aiki a banza? Faɗa mini abin da albashinka zai zama.”
16
Laban dai yana da ’ya’ya mata biyu; sunan babbar Liyatu, sunan ƙaramar kuwa Rahila.
Settings