Tsallake zuwa abun ciki
Farawa 20:14-16

An mayar wa Saratu; Abimelek ya biya diyya

Farawa 20:14-16
14
Sai Abimelek ya kawo awaki da shanu da bayi maza da mata, ya ba wa Ibrahim, ya kuma komar da Saratu matarsa gare shi.
15
Abimelek ya kuma ce, “Ƙasata tana gabanka, ka zauna a duk inda kake so.”
16
Ga Saratu kuwa ya ce, “Ina ba wa ɗan’uwanki shekel dubu na azurfa, shaida ce ta tabbatarwa a idanun dukan waɗanda suke tare da ke, da kuma a gaban kowa cewa ba ki da laifi.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options