Farawa 15:15-21
15
Amma kai za ka koma wurin kakanninka cikin salama a kuma binne ka da kyakkyawan tsufa.
16
A tsara ta huɗu zuriyarka za tă komo nan, saboda zunubin Amoriyawa bai riga ya cika ba.”
17
Sa’ad da rana ta fāɗi, aka kuwa yi duhu, sai wata tukunya mai hayaƙi, mai harshen wuta mai ci, ta bayyana, ta kuma wuce tsakanin abubuwan nan da aka tsaga.
18
A wannan rana, Ubangiji ya yi alkawari da Abram ya ce, “Ga zuriyarka na ba da wannan ƙasa, daga kogin Masar zuwa babban kogi, Yuferites ke nan,
19
ƙasar Keniyawa, Kenizziyawa, Kadmoniyawa,
20
Hittiyawa, Ferizziyawa, Refahiyawa,
21
Amoriyawa, Kan’aniyawa, Girgashiyawa da kuma Yebusiyawa.”
Settings