Ezekiyel 48:30-35
30
“Waɗannan za su zama ƙofofin birnin. “Farawa da gefen arewa, wanda yake da tsawon kamu 4,500
31
za a ba wa ƙofofin birnin sunaye kabilan Isra’ila. Ƙofofi uku a gefen arewa za su zama ƙofar Ruben, ƙofar Yahuda da ƙofar Lawi.
32
A gefen gabas, wanda yake da tsawon kamu 4,500 zai kasance da ƙofofi uku, ƙofar Yusuf, ƙofar Benyamin da ƙofar Dan.
33
A gefen kudu, wanda yake da tsawon kamu 4,500, zai kasance da ƙofofi uku, ƙofar Simeyon, ƙofar Issakar da ƙofar Zebulun.
34
A gefen yamma, wanda yake da tsawon kamun 4,500, zai kasance da ƙofofi uku, ƙofar Gad, ƙofar Asher da kuma ƙofar Naftali.
35
“Duk nisan wurare kewaye da birnin zai zama kamu 18,000 ne. “Sunan birnin kuwa daga wannan lokaci zai zama, ‘Ubangiji yana a nan.’ ”
Settings