Skip to content
Ezekiyel 48:23-29

Ezekiyel 48:23-29

23
“Game da sauran kabilun kuwa, “Benyamin zai sami rabo; zai miƙe daga wajen gabas zuwa wajen yamma.
24
Simeyon zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Benyamin daga gabas zuwa yamma.
25
Issakar zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Simeyon daga gabas zuwa yamma.
26
Zebulun zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Issakar daga gabas zuwa yamma.
27
Gad zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Zebulun daga gabas zuwa yamma.
28
Iyakar kudu ta Gad za tă miƙe kudu daga Tamar zuwa ruwan Meriba Kadesh, sa’an nan ta bi Rafin Masar zuwa Bahar Rum.
29
“Wannan ce ƙasar da za ku raba gādo ga kabilan Isra’ila, kuma wannan ne zai zama rabonsu,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options