Ezekiyel 44:1-8
1
Sai mutumin ya komo da ni zuwa ƙofar waje na wuri mai tsarki, wadda take fuskantar gabas, tana kuwa a rufe.
2
Ubangiji ya ce mini, “Wannan ƙofar za tă kasance a rufe. Ba za a buɗe ta ba; ba wanda zai shiga ta wurinta. Za tă kasance a rufe domin Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya shiga ta wurinta.
3
Sarki kansa ne kaɗai zai zauna a hanyar shiga don yă ci a gaban Ubangiji. Zai shiga ta hanyar shirayin hanyar shiga yă kuma fita a wannan hanya.”
4
Sa’an nan mutumin ya kawo ni ta hanyar ƙofar arewa zuwa gaban haikali. Na duba na kuma ga ɗaukakar Ubangiji tana cika haikalin Ubangiji, sai na fāɗi rubda ciki.
5
Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, ka lura sosai, ka saurara sosai ka kuma mai da hankali ga kome da na faɗa maka game da dukan ƙa’idodi game da haikalin Ubangiji. Ka lura sosai da ƙofar shigar haikali da kuma dukan ƙofofin wuri mai tsarki.
6
Faɗa wa ’yan tawayen gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ayyukan banƙyamarku sun isa haka, ya gidan Isra’ila!
7
Ban da dukan sauran ayyukanku na banƙyama, kun kawo baƙi marasa kaciya a zuciya da jiki a wurina mai tsarki, kun kuma ƙazantar da haikalina yayinda kuke miƙa mini abinci, kitse da kuma jini, kun kuma karya alkawarina.
8
A maimakon yin ayyukanku bisa ga abubuwana masu tsarki, kun sa waɗansu su lura da wurina mai tsarki.
Settings