Skip to content
Ezekiyel 41:16-26

Ezekiyel 41:16-26

16
da madogaran ƙofa da matsattsun tagogi da rumfuna kewaye da su ukun, har da kome da yake gaba haɗe da madogarar ƙofa, an rufe su da katako. An rufe bangon haikalin daga ƙasa har zuwa tagogi, tagogin kuwa an rufe su.
17
A filin da yake bisan ƙofar shiga na waje zuwa wuri mai tsarki na can ciki da kuma a bangayen da aka daidaita tsakani kewaye da wuri mai tsarki na can ciki da kuma na can waje
18
an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino. Zānen siffar itacen dabino yana a tsakanin kerub da kerub. Kowane kerub yana da fuska biyu,
19
fuskar ɗaya kamar ta mutum tana fuskantar zānen siffar itacen dabino a wannan gefe, ɗaya fuskar kamar ta zaki tana fuskantar zānen siffar itacen dabino na wancan gefe. Haka aka zāna su dukan a jikin bangon haikalin kewaye.
20
Daga ƙasa zuwa daurin ƙofa, an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino a waje na wuri mai tsarki.
21
Wuri mai tsarki da yake waje yana da madogarar ƙofa murabba’i, haka ma wadda take a gaban Wuri Mafi Tsarki.
22
Akwai bagaden katako mai tsayi kamu uku, fāɗinsa kamu biyu da kuma tsawonsa kamu biyu; kusurwansa, tushensa da kuma gefe-gefensa duk katako ne. Sai mutumin ya ce mini, “Wannan shi ne tebur da yake a gaban Ubangiji.”
23
A wuri mai tsarki da yake waje da kuma Wuri Mafi Tsarki suna da ƙofa biyu a haɗe.
24
Kowace ƙofa tana da murfi biyu masu buɗewa ciki da waje.
25
A ƙofofin wuri mai tsarki da yake waje an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino kamar yadda aka zāna a bangayen, akwai kuma rumfar da aka yi da itace a gaban shirayin.
26
A bangayen da suke gefen shirayin akwai matsattsun tagogi da aka zāna siffar itatuwan dabino a kowane gefe. Gefe-gefen ɗakunan haikalin ma suna da rumfuna.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options