Ezekiyel 41:12-15
12
Faɗin ginin da yake fuskantar filin haikali a wajen yamma kamu saba’in ne. Kaurin bangon ginin kamu biyar ne kewaye, tsawonsa kuma kamu tasa’in ne.
13
Sa’an nan ya auna haikalin; tsawonsa kamu ɗari ne, tsawon filin haikalin da ginin tare da bangayensa su ma kamu ɗari ne.
14
Faɗin filin haikalin a wajen gabas, haɗe da gaban haikalin, kamu ɗari ne.
15
Sa’an nan ya auna tsawon ginin da yake fuskantar filin a bayan haikalin, haɗe da rumfunansa a kowane gefe, kamu ɗari. Wuri mai tsarki da yake waje, wuri mai tsarki da yake can ciki da shirayin da yake fuskantar filin,
Settings