Tsallake zuwa abun ciki
Ezekiyel 35:10-15

Girman kan Edom da kufansa na ƙarshe

Ezekiyel 35:10-15
10
“ ‘Domin kun ce, “Waɗannan al’ummai biyu da ƙasashe za su zama namu za mu kuma mallake su,” ko da yake Ni Ubangiji ina a can,
11
saboda haka muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan sāka maka gwargwadon fushi da kuma kishin da ka nuna a ƙiyayyarsu da ka yi zan kuma sanar da kaina a cikinsu sa’ad da na hukunta ka.
12
Sa’an nan za ka san cewa Ni Ubangiji na ji duk abubuwan banzan da ka faɗa a kan duwatsun Isra’ila. Ka ce, “An mai da su kango an kuma ba mu su mu cinye.”
13
Ka yi fariya a kaina, ka kuma yi magana a kaina ba gaggautawa, na ji shi sarai.
14
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa yayinda dukan duniya take farin ciki, zan mai da kai kango.
15
Domin ka yi farin ciki sa’ad da gādon gidan Isra’ila ya zama kufai, haka zan yi da kai, ya Dutsen Seyir, kai da dukan Edom. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options