Ezekiyel 35:5-9
5
“ ‘Domin ka riƙe ƙiyayya ta tun dā, ka kuma ba da mutanen Isra’ila domin a kashe su da takobi a lokacin masifarsu, lokacin da adadin horonsu ya cika,
6
saboda haka muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan sa a zub da jininka zan kuwa fafare ka. Da yake ba ka ƙi zub da jini ba, zub da jini zai fafare ka.
7
Zan mai da Dutsen Seyir kango in kuma yanke dukan waɗanda suke shiga da fita a cikinka.
8
Zan cika duwatsunka da matattu; waɗanda aka kashe da takobi za su fāɗi a kan tuddanka, da cikin kwarurukanka, da cikin dukan kwazazzabanka.
9
Zan mai da kai kango har abada; ba za a zauna a cikin garuruwanka ba. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.
Settings