Skip to content
Ezekiyel 35:1-4

Ezekiyel 35:1-4

1
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2
“Ɗan mutum, ka fuskanci Dutsen Seyir; ka yi annabci a kansa
3
ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, Dutsen Seyir, zan kuma miƙa hannuna gāba da kai in mai da kai kango.
4
Zan mai da garuruwanka kufai za ka kuma zama kango. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options