Ezekiyel 33:1-20
1
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2
“Ɗan mutum, yi magana da mutanen ƙasarka ka faɗa musu cewa, ‘Sa’ad da na kawo takobi a kan ƙasar, mutanen ƙasar kuwa suka zaɓi ɗaya daga cikin mutanensu suka mai da shi mai tsaro,
3
ya kuma ga takobi yana zuwa a kan ƙasar ya kuwa busa ƙaho don yă faɗakar da mutane,
4
in wani ya ji busar amma bai kula ba, takobin zai zo ya ɗauki ransa, jininsa kuwa zai zauna a kansa.
5
Da yake ya ji ƙarar busar amma bai kula ba, jininsa zai zauna a kansa. Da a ce ya kula, da ya ceci kansa.
6
Amma a ce mai tsaron ya ga takobi yana zuwa bai kuwa busa ƙaho don yă faɗakar da mutane ba sai takobi ya zo ya ɗauki ran waninsu, za a kawar da wannan mutum saboda zunubinsa, amma zan nemi hakkin jinin mutumin a kan mai tsaron.’
7
“Ɗan mutum, na mai da kai mai tsaro bisa gidan Isra’ila; saboda haka ka ji abin da zan faɗa ka kuma gargaɗe su.
8
Sa’ad da na ce wa mugu, ‘Ya mugun mutum, tabbatacce za ka mutu,’ kai kuma ba ka yi magana don ka juyar da shi daga hanyoyinsa ba, wannan mugun mutum zai mutu domin zunubinsa, zan kuma nemi hakkin jininsa a kanka.
9
Amma in ka faɗakar da mugun mutumin don yă juye daga hanyoyinsa bai kuwa yi haka ba, zai mutu saboda zunubinsa, amma kai za ka kuɓutar da kanka.
10
“Ɗan mutum, faɗa wa gidan Isra’ila, ‘Ga abin da kuke cewa, “Laifofinmu da zunubanmu suna nawaita mana, muna kuma lalacewa saboda su. Ta ƙaƙa za mu rayu?” ’
11
Ka faɗa musu, ‘Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba na jin daɗin mutuwar mugu, amma a maimako haka ya fi su juye daga hanyoyinsu su rayu. Ku juye! Ku juye daga mugayen hanyoyinku! Don me za ku mutu, ya gidan Isra’ila?’
12
“Saboda haka, ɗan mutum, ka faɗa wa mutanen ƙasarka, ‘Adalcin adali ba zai cece shi sa’ad da ya ƙi yin biyayya ba, kuma muguntar mugu ba za tă sa ya fāɗi sa’ad da ya juya daga gare ta ba. Adali, in ya yi zunubi, ba za a bari yă rayu saboda adalcinsa na dā ba.’
13
In na faɗa wa adali cewa tabbatacce zai rayu, amma sai ya dogara ga adalcinsa ya kuma aikata mugunta, babu ayyukan adalcinsa da za a tuna; zai mutu saboda muguntar da ya aikata.
14
Kuma in na ce wa mugu, ‘Tabbatacce za ka mutu,’ amma sai ya juye daga zunubinsa ya kuma yi abin da yake gaskiya da kuma daidai,
15
in ya mayar da jingina, ya mayar da abin da ya sata, ya kiyaye ƙa’idodin da suke ba da rai, ya daina yin mugunta, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba.
16
Babu wani zunubin da ya aikata da za a tuna da shi. Ya yi abin da yake gaskiya da kuma daidai; tabbatacce zai rayu.
17
“Duk da haka mutanen ƙasarka sun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Alhali kuwa tasu ce ba daidai ba.
18
In adali ya juye daga adalcinsa ya yi mugunta, zai mutu saboda haka.
19
Kuma in mugu ya juye daga muguntarsa ya aikata abin da yake gaskiya da kuma daidai, zai rayu ta yin haka.
20
Duk da haka, ya gidan Isra’ila kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Amma zan hukunta kowane ɗayanku gwargwadon ayyukansa.”
Settings