Skip to content
Ezekiyel 27:3

Ezekiyel 27:3

Ana nuna aya 3 tare da mahallin da ke kewaye.
1
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2
“Ɗan mutum, ka yi makoki domin Taya.
3
Ka ce wa Taya, wadda take zaune a hanyar shiga zuwa teku, kasuwar masu yawa mutane a bakin teku, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Kin ce, ya Taya, “Ni kyakkyawa ce cikakkiya.”
4
Manyan tekuna ne wurin zamanki; maginanki sun sa kyanki ya zama cikakke.
5
Sun yi dukan katakanki daga itatuwan fir daga Senir; sun kwaso itatuwan al’ul daga Lebanon don su yi miki jigon jirgin ruwa.
6
Da oak daga Bashan suka yi sandunan tuƙan jirgin ruwa da itatuwan kasharina daga bakin tekun Saifurus suka yi daɓe jirgin ruwanki, suka kuma manne masa hauren giwa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options