Skip to content
Ezekiyel 27:5-11

Ezekiyel 27:5-11

5
Sun yi dukan katakanki daga itatuwan fir daga Senir; sun kwaso itatuwan al’ul daga Lebanon don su yi miki jigon jirgin ruwa.
6
Da oak daga Bashan suka yi sandunan tuƙan jirgin ruwa da itatuwan kasharina daga bakin tekun Saifurus suka yi daɓe jirgin ruwanki, suka kuma manne masa hauren giwa.
7
Lilin mai kyau mai ado daga Masar ne filafilan jirgin ruwanki suka kuma zama tutarki; an yi tutarki da shuɗi da shunayya daga bakin tekun Elisha.
8
Mutanen Sidon da Arfad su ne matuƙan jirgin ruwanki; gwanayenki, ya Taya, suna ciki a matsayi matuƙan jiragen ruwa.
9
Masu hikima na Gebal suna ciki a matsayin masu tattoshe mahaɗan katakon jirginki. Dukan jiragen ruwa da matuƙansu sukan zo wurinki don kasuwanci.
10
“ ‘Mutanen Farisa, Lidiya da Fut su ne suka zama sojoji a cikin mayaƙanki. Sun rataye garkuwoyinsu da hulunan kwano a katangarki, suna kawo miki daraja.
11
Mutanen Arfad da Helek sun yi tsaron katangar a kowace gefe; mutanen Gammad su ne a hasumiyoyinki. Sun rataye garkuwoyinsu kewaye da katangarki; sun sa kyanki ya zama cikakke.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options