Skip to content
Ezekiyel 20:1-27

Ezekiyel 20:1-27

1
A shekara ta bakwai, a wata na biyar a rana ta goma, waɗansu dattawan Isra’ila suka zo don su nemi nufin Ubangiji, suka kuwa zauna a ƙasa a gabana.
2
Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
3
“Ɗan mutum, ka yi magana da dattawan Isra’ila ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kun zo ne ku nemi shawarata? Muddin ina raye, ba zan bari ku nemi shawarata ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’
4
“Za ka hukunta su? Za ka hukunta su, ɗan mutum? To, sai ka kalubalance su da ayyukan banƙyamar kakanninsu
5
ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar da na zaɓi Isra’ila, na ɗaga hannuna, na rantse wa zuriyar gidan Yaƙub na kuma bayyana kaina gare su a Masar da hannun da na ɗaga na ce musu, “Ni ne Ubangiji Allahnku.”
6
A ranar na yi musu rantsuwa cewa zan fitar da su daga Masar zuwa ƙasar da na samo musu, ƙasa mai zub da madara da zuma, ƙasa mafi kyau cikin dukan ƙasashe.
7
Na kuma ce musu, “Kowannenku ya zubar da mugayen siffofin da kuka kafa idanunku a kai, kuma kada ku ƙazantar da kanku da gumakan Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.”
8
“ ‘Amma sai suka yi tawaye a kaina ba su kuwa saurare ni ba; ba su zubar da mugayen siffofin da suka kafa idanunsu a kai ba, balle su ƙi gumakan Masar. Saboda haka zan zubo hasalata a kansu in kuma aukar musu da fushina a Masar.
9
Amma saboda sunana na yi abin da zai kiyaye shi daga ƙazantuwa a idanun al’umman da suka zauna a ciki da kuma a idanun al’ummai da na bayyana kaina ga Isra’ilawa ta wurin fitar da su daga Masar.
10
Saboda haka na fisshe su daga Masar na kawo su cikin hamada.
11
Na ba su ƙa’idodina na kuma sanar musu da dokokina, gama mutumin da ya yi biyayya da su zai rayu ta wurinsu.
12
Na kuma ba su Asabbataina kamar alama tsakaninmu, domin su san cewa Ni Ubangiji ne yake tsarkake su.
13
“ ‘Duk da haka mutanen Isra’ila suka yi mini tawaye a cikin hamada. Ba su bi ƙa’idodina ba amma suka ki dokokina, ko da yake mutumin da ya yi biyayya da su zai rayu ta wurinsu, suka ɓata Asabbataina ƙwarai. Saboda haka na ce zan zuba hasalata a kansu in kuma hallaka su a hamada.
14
Amma saboda sunana na yi abin da zai kiyaye shi daga ƙazantuwa a idanun al’umman da a idonsu na fisshe su.
15
Na kuma ɗaga hannu na rantse musu a hamada cewa ba zan kawo su ƙasar da na ba su ba, ƙasa mai zub da madara da zuma, ƙasa mafi kyau cikin dukan ƙasashe,
16
domin sun ƙi dokokina ba su kuwa bi ƙa’idodina ba suka kuma ƙazantar da Asabbataina. Gama zukatansu sun fi so su bauta wa gumakansu.
17
Duk da haka na dube su ta tausayi ba zan hallaka su ko in kawo ƙarshensu a hamada ba.
18
Na faɗa wa ’ya’yansu a hamada, “Kada ku bi farillai kakanninku ko ku kiyaye dokokinsu ko ku ƙazantar da kanku da gumakansu.
19
Ni ne Ubangiji Allahnku; ku bi ƙa’idodina ku kuma kula ku kiyaye dokokina.
20
Ku kiyaye Asabbataina da tsarki, don su zama alama tsakaninmu. Ta haka za ku san cewa ni ne Ubangiji Allahnku.”
21
“ ‘Amma ’ya’yan suka yi mini tawaye. Ba su bi ƙa’idodina ba, ba su kula su kiyaye dokokina ba, ko da yake mutumin da ya kiyaye su zai rayu ta wurinsu, suka kuma ƙazantar da Asabbataina. Saboda haka na ce zan zuba hasalata a kansu in kuma aukar musu da fushina a hamada.
22
Amma na janye hannuna, kuma saboda sunana na yi abin da zai kiyaye shi daga ƙazantuwa a idanun al’umman da a idonsu na fisshe su.
23
Na kuma ɗaga hannu na rantse musu cewa zan watsar da su cikin al’ummai in kuma warwatsa su cikin ƙasashe,
24
domin ba su kiyaye dokokina ba amma suka ƙi ƙa’idodina suka kuma ƙazantar da Asabbataina, idanunsu suka yi sha’awar gumakan kakanninsu.
25
Na kuma ba da su ga farillan da ba su da kyau da dokokin da ba za su rayu ta wurinsu ba;
26
na bari suka ƙazantu ta wurin kyautai, hadayar kowane ɗan fari don in cika su da abin tsoro domin su san cewa ni ne Ubangiji.’
27
“Saboda haka, ɗan mutum, ka yi magana da mutanen Isra’ila ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a wannan kuma kakanninku suka saɓe ni ta wurin yashe ni.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options