Ezekiyel 19:10-14
10
“ ‘Mahaifiyarku kamar kuringa ce a cikin gonar inabi da aka shuka kusa da ruwa; ta ba da ’ya’ya da kuma cikakkun rassa saboda yalwan ruwa.
11
Rassanta suka yi ƙarfi, suka dace da sandar mai mulki. Ta yi tsayi zuwa sama ana ganin ta saboda tsayinta da kuma saboda yawan rassanta.
12
Amma aka tumɓuke ta cikin fushi aka jefar da ita a ƙasa. Iskar gabas ta sa ta yanƙwane, aka kakkaɓe ’ya’yanta; rassanta masu ƙarfi suka bushe wuta kuma ta cinye su.
13
Yanzu an shuka ta a hamada, a busasshiyar ƙasa marar ruwa.
14
Wuta ta fito daga jikin rassanta ta cinye ’ya’yanta. Babu sauran reshe mai ƙarfin da ya rage a kanta da ya dace da sandar mai mulki.’ Wannan waƙa ce kuma za a yi amfani da ita a matsayin makoki.”
Settings