Skip to content
Ezekiyel 19:1-9

Ezekiyel 19:1-9

1
“Ka yi makoki game da sarakunan Isra’ila
2
ka ce, “ ‘Mahaifiyarki zakanya ce cikin zakoki! Takan kwanta cikin ’yan zakoki ta kuma yi renon kwiyakwiyanta.
3
Ta goyi ɗaya daga cikin kwiyakwiyanta, ya yi girma ya zama zaki mai ƙarfi. Ya koyi yayyage abin da ya yi farauta yakan kuma cinye mutane.
4
Al’ummai suka ji labarinsa, aka kuma kama shi cikin raminsu. Suka ja shi da ƙugiyoyi zuwa ƙasar Masar.
5
“ ‘Sa’ad da ta ga sa zuciyarta bai cika ba, abin da take fata gani ya tafi, sai ta ɗauki wani daga cikin kwiyakwiyanta ta mai da shi zaki mai ƙarfi.
6
Ya yi ta yawo a cikin zakoki, gama yanzu shi zaki ne mai ƙarfi. Ya koyi yayyage abin da ya yi farauta yakan kuma cinye mutane.
7
Ya rurrushe kagaransu ya kuma ragargaza biranensu. Ƙasar da dukan waɗanda suke cikinta sun tsorata da jin rurinsa.
8
Sai al’ummai suka tayar masa, waɗannan daga yankunan da suke kewaye. Suka yafa raga dominsa ya kuwa fāɗa cikin raminsu.
9
Da ƙugiyoyi suka ja shi cikin keji suka kawo shi wurin sarkin Babilon. Suka sa shi cikin kurkuku, saboda haka ba a ƙara jin rurinsa a kan duwatsun Isra’ila ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options