- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Makoki saboda sarakunan Isra’ila
Ezekiyel 19:1-9
1
“Ka yi makoki game da sarakunan Isra’ila
2
ka ce, “ ‘Mahaifiyarki zakanya ce cikin zakoki! Takan kwanta cikin ’yan zakoki ta kuma yi renon kwiyakwiyanta.
3
Ta goyi ɗaya daga cikin kwiyakwiyanta, ya yi girma ya zama zaki mai ƙarfi. Ya koyi yayyage abin da ya yi farauta yakan kuma cinye mutane.
4
Al’ummai suka ji labarinsa, aka kuma kama shi cikin raminsu. Suka ja shi da ƙugiyoyi zuwa ƙasar Masar.
5
“ ‘Sa’ad da ta ga sa zuciyarta bai cika ba, abin da take fata gani ya tafi, sai ta ɗauki wani daga cikin kwiyakwiyanta ta mai da shi zaki mai ƙarfi.
6
Ya yi ta yawo a cikin zakoki, gama yanzu shi zaki ne mai ƙarfi. Ya koyi yayyage abin da ya yi farauta yakan kuma cinye mutane.
7
Ya rurrushe kagaransu ya kuma ragargaza biranensu. Ƙasar da dukan waɗanda suke cikinta sun tsorata da jin rurinsa.
8
Sai al’ummai suka tayar masa, waɗannan daga yankunan da suke kewaye. Suka yafa raga dominsa ya kuwa fāɗa cikin raminsu.
9
Da ƙugiyoyi suka ja shi cikin keji suka kawo shi wurin sarkin Babilon. Suka sa shi cikin kurkuku, saboda haka ba a ƙara jin rurinsa a kan duwatsun Isra’ila ba.
Settings