Skip to content
Ezekiyel 18:26-30

Ezekiyel 18:26-30

26
In mai adalci ya juye daga adalcinsa ya yi zunubi, zai mutu saboda wannan; saboda zunubin da ya yi, zai mutu.
27
Amma in mugun mutum ya juye daga muguntarsa ya kuma yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, zai ceci ransa.
28
Domin ya lura da dukan laifofin da ya yi ya kuma juye daga gare su, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba.
29
Duk da haka mutanen Isra’ila sun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Hanyoyina ba daidai ba ne, ya gidan Isra’ila? Ba hanyoyinku ne ba daidai ba?
30
“Saboda haka, ya gidan Isra’ila, zan hukunta ku, kowa bisa ga hanyarsa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tuba! Ku juye daga dukan laifofinku; sa’an nan zunubi ba zai zama sanadin fāɗuwarku ba.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options