Ezekiyel 18:1-11
1
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2
“Me ku mutane kuke nufi da faɗar wannan karin magana a kan ƙasar Isra’ila cewa, “ ‘Ubanni sun ci ’ya’yan inabi masu tsami, haƙoran ’ya’ya kuwa sun mutu’?
3
“Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba za ku ƙara faɗar wannan karin magana a Isra’ila ba.
4
Gama kowane mai rai nawa ne, mahaifi da ɗa, duk nawa ne. Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu.
5
“A ce akwai mai adalci wanda yake aikata abin da yake daidai da kuma gaskiya;
6
ba ya cin abinci a duwatsun tsafi ko ya dogara ga gumakan gidan Isra’ila. Ba ya ƙazantar da matar maƙwabcinsa ko ya kwana da mace lokacin al’adarta ba.
7
Ba ya cin zalin wani, amma yakan mayar wa wanda ya ba shi jingina abin da ya jinginar masa. Ba ya yi fashi amma yakan ba wa mayunwata abinci ya kuma tanada wa marasa tufafi riga.
8
Ba ya ba da bashi da ruwa ko ya karɓa ƙarin riba. Yakan janye hannunsa daga aikata mugunta yakan kuma yi shari’a cikin gaskiya tsakanin mutum da mutum.
9
Yana bin ƙa’idodina yana kuma kiyaye dokokina da aminci. Wannan mutumin adali ne; tabbatacce zai rayu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
10
“A ce yana da ɗa wanda yana kisa ko yana yin ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa
11
(ko da yake mahaifin bai yi ko ɗaya daga cikinsu ba). “Yakan ci abinci a duwatsun tsafi. Yakan ƙazantar da matar maƙwabci.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings