Ezekiyel 16:48-52
48
Muddin in raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ’yar’uwarki Sodom da ’ya’yanta mata ba su yi abin da ’ya’yanki mata suka yi ba.
49
“ ‘To, fa, ga zunubin ’yar’uwarki Sodom. Ita da ’ya’yanta mata sun yi girman kai, sun ƙoshi fiye da kima kuma ba su kula da wani abu ba; ba su taimaki matalauta da kuma masu bukata ba.
50
Su masu girman kai ne kuma suka aikata abubuwa masu banƙyama a gabana. Saboda haka na kau da su kamar yadda ka gani.
51
Samariya ba tă aikata ko rabin zunubanki ba. Kin aikata abubuwa masu banƙyama fiye da su, suka kuma sa ’yan’uwanki mata suka zama kamar masu adalci ta wurin dukan waɗannan abubuwa da kika aikata.
52
Ki sha kunyarki, gama kin yi rangwame wa ’yan’uwanki mata. Saboda zunubanki sun yi muni fiye da nasu, sai suka zama kamar sun fi ki adalci. Saboda haka, ki sha kunya ki kuma sha ƙasƙancinki, gama kin sa ’yan’uwanki mata suka zama kamar su masu adalci ne.
Settings