Fitowa 9:18-26
18
Saboda haka, gobe war haka, zan sa a yi ƙanƙara mai tsananin gaske, irin wadda Masar ba tă taɓa gani ba tun kahuwarta, har yă zuwa yanzu.
19
Yanzu, ka ba da umarni a dawo da shanunku da kuma kome da kuke da shi wanda yake a gona zuwa gida, gama ƙanƙarar za tă kashe kowane mutum ko dabba wadda take a gona wadda ba a kawo cikin gida ba, sa’ad da ta fāɗo.’ ”
20
Waɗansu daga cikin dattawan Fir’auna suka cika da tsoro saboda abin da Ubangiji ya faɗa, nan da nan suka shigo da dabbobinsu da bayinsu da sauri daga gona zuwa cikin gida.
21
Amma waɗanda ba su kula da maganar Ubangiji ba, suka bar bayinsu da dabbobi a gona.
22
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama don a yi ƙanƙara a bisa dukan Masar, a bisa mutane da dabbobi, da bisa dukan abubuwan da suke girma a gonakin Masar.”
23
Da Musa ya miƙa sandansa sama, sai Ubangiji ya aiko da tsawa da ƙanƙara, da walƙiya har ƙasa. Ta haka Ubangiji ya yi ruwan ƙanƙara a bisa ƙasar Masar;
24
ƙanƙara ta fāɗo, walƙiya kuma tana ta wulƙawa. Wannan ce ƙanƙara mafi munin da aka taɓa yi, a dukan ƙasar Masar, tun tarihin kahuwarta na zaman al’umma.
25
Ko’ina a Masar ƙanƙara ta bugi duk abin da yake a gonaki, mutane da dabbobi, ta bugi duk ganyaye da suke a gonaki, ta kuma ragargaza kowane itace.
26
Wuri guda kaɗai da ba a yi ruwan ƙanƙara ba, shi ne yankin Goshen, inda Isra’ilawa suke.
Settings