Fitowa 4:27-31
27
Ubangiji ya ce wa Haruna, “Tafi cikin hamada ka sadu da Musa.” Sai ya sadu da Musa a dutsen Allah, ya sumbace shi.
28
Sai Musa ya gaya wa Haruna dukan abin da Ubangiji ya aike yă faɗa, da kuma dukan mu’ujizan da ya umarce shi yă aikata.
29
Musa da Haruna suka tattara dukan dattawan Isra’ilawa,
30
sai Haruna ya gaya musu dukan abin da Ubangiji ya ce wa Musa. Ya kuma aikata mu’ujizan a gaban mutanen,
31
sai suka gaskata. Sa’ad da suka ji cewa Ubangiji ya damu da su, ya kuma ga azabarsu, sai suka durƙusa suka yi sujada.
Settings