Fitowa 5:1-5
1
Daga bisani sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna suka ce, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Bari mutanena su tafi domin su yi mini biki a hamada.’ ”
2
Fir’auna ya ce, “Wane ne Ubangiji da zan yi biyayya da shi, har in bar Isra’ila su tafi? Ban san Ubangiji ba, kuma ba zan bar Isra’ila su tafi ba.”
3
Sai suka ce, “Allah na Ibraniyawa ya sadu da mu. Yanzu bari mu ɗauki tafiyar kwana uku cikin hamada domin mu miƙa hadaya ga Ubangiji Allahnmu, don kada yă buga mu da annoba ko takobi.”
4
Amma sarkin Masar ya ce wa, “Musa da Haruna, don me kuke hana mutane yin aikinsu? Ku koma wurin aikinku!”
5
Sa’an nan Fir’auna ya ce, “Ga shi mutane sun yi yawa a ƙasar Masar, ku kuma yanzu kuna so ku hana su yin aiki.”
Settings