Fitowa 36:31-33
31
Suka kuma yi sanduna na itace ƙirya, biyar domin katakan da suke a gefe guda na tabanakul,
32
biyar domin waɗanda suke ɗayan gefen da kuma biyar domin katakan da suke gefen yamma na iyaka ta ƙarshen tabanakul.
33
Suka sa sandan da yake a tsakiya yă wuce daga wannan gefe zuwa wancan.