Tsallake zuwa abun ciki
Fitowa 19:3-8

Allah ya gabatar da alkawari

Fitowa 19:3-8
3
Sai Musa ya hau kan dutsen don yă sadu da Allah, Ubangiji kuwa ya kira shi daga dutsen ya ce, “Wannan shi ne abin da za ka faɗa wa gidan Yaƙub, da kuma abin da za ka faɗa wa mutanen Isra’ila.
4
‘Ku da kanku kun ga abin da na yi wa Masar, da yadda na ɗauko ku a kan fikafikan gaggafa na kawo ku wurina.
5
Yanzu, in kuka yi mini cikakken biyayya, kuka kuma kiyaye yarjejjeniyata, to, za ku zama keɓeɓɓiyar taska a gare ni a cikin dukan al’ummai. Ko da yake duk duniya tawa ce,
6
za ku zama firistoci masu tsarki da kuma al’umma keɓaɓɓiya a gare ni.’ Waɗannan su ne kalmomin da za ka faɗa wa Isra’ilawa.”
7
Sai Musa ya koma ya aika a kira dukan dattawan mutane, ya bayyana dukan kalmomin da Ubangiji ya umarta, ya faɗa.
8
Dukan mutane suka amsa gaba ɗaya suka ce, “Za mu yi duk abin da Ubangiji ya faɗa.” Sai Musa ya mayar wa Ubangiji amsar da mutane suka bayar.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options