Fitowa 13:17-22
17
Sa’ad da Fir’auna ya bar mutane su tafi, Allah bai bi da su a hanyar da ta bi ta iyakar Filistiyawa ba, ko da yake wannan hanya ce ta fi kusa. Gama Allah ya ce, “In suka fuskanci yaƙi, wataƙila su canja ra’ayinsu su koma Masar.”
18
Saboda haka Allah ya kewaye da mutanen ta hamada zuwa Jan Teku. Isra’ilawa kuwa suka fita daga Masar da shirin yaƙi.
19
Musa ya ɗauki ƙasusuwan Yusuf tare da shi, gama Yusuf ya sa Isra’ilawa su rantse masa. Ya ce, “Tabbatacce Allah zai taimake ku, sai ku ɗibi ƙasusuwana tare da ku daga wannan wuri.”
20
Bayan sun bar Sukkot sai suka kafa sansani a Etam a bakin hamada.
21
Da rana Ubangiji yakan ja gabansu a cikin al’amudin girgije domin yă bishe su a kan hanyarsu, da dare kuma a cikin al’amudin wuta domin yă ba su haske, domin su iya tafiya dare da rana.
22
Al’amudan nan biyu, na girgije da na wuta, ba su daina yi wa jama’a jagora ba.
Settings