Fitowa 11:3-7
3
(Ubangiji ya sa mutane suka sami tagomashi a idon Masarawa, Musa kuwa ya sami girma sosai a cikin ƙasar Masar a gaban fadawan Fir’auna da kuma a gaban jama’ar.)
4
Saboda haka Musa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Wajen tsakar dare, zan ratsa dukan Masar.
5
Kowane ɗan fari, namiji, a Masar zai mutu, daga kan ɗan fari na Fir’auna wanda zai ci gadon sarauta, har zuwa kan ɗan fari na baiwa, wadda take niƙa, da kuma dukan ’yan farin shanu.
6
Za a yi kuka mai zafi ko’ina a Masar, irin wadda ba a taɓa yi ba, ba kuwa za a ƙara yi ba.
7
Amma a cikin Isra’ilawa, ba karen da zai yi haushi wa mutum ko dabba.’ Ta haka za ku sani Ubangiji zai bambanta tsakanin Masar da Isra’ila.
Settings