Esta 8:3-8
3
Esta ta sāke roƙon sarki, ta fāɗi a ƙafafunsa tana kuka. Ta roƙe shi yă kawo ƙarshen mugun shirin nan na Haman, mutumin Agag; wanda ya shirya a kan Yahudawa.
4
Sai sarki ya miƙa wa Esta sandan sarauta na zinariya, ta kuwa tashi ta tsaya a gabansa.
5
Ta ce, “In sarki ya yarda, in kuma na sami tagomashi daga gare shi, idan kuma ya gamshe shi yă yi abin da yake daidai, idan yana jin daɗina, bari a rubuta umarni a soke hukuncin saƙonin da Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, ya shirya ya kuma rubuta domin a hallaka Yahudawa a dukan lardunan sarki.
6
Gama yaya zan jure da ganin masifa ta faɗa a kan mutanena? Yaya zan jure in ga an hallaka iyalina?”
7
Sarki Zerzes ya amsa wa Esta da Mordekai mutumin Yahuda, “Domin Haman ya kai wa Yahudawa hari, na ba da mallakarsa ga Esta, an kuma rataye shi a wurin rataye mai laifi.
8
Yanzu ku rubuta wata doka, a sunan sarki, a madadin Yahudawa, yadda kuka ga ya fi kyau ku kuma hatimce ta da zoben hatimin sarki, gama babu takardar da aka rubuta da sunan sarki, aka kuma hatimce da zobensa da za a iya sokewa.”
Settings