Esta 6:6-11
6
Sa’an nan Haman ya shigo, sai sarki ya ce masa, “Me ya kamata a yi wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama?” Haman dai ya yi tunani a ransa ya ce, “Wane ne sarki zai girmama in ba ni ba?”
7
Sai ya amsa wa sarki cewa, “Saboda mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama,
8
bari a kawo rigar sarautar da sarki ya taɓa sawa, da kuma dokin da sarki ya taɓa hawa, wanda aka sa kambin sarauta a kai.
9
Sa’an nan, bari a ba da rigar da kuma dokin wa ɗaya daga cikin manyan sarakuna mafi kirki na sarki. Bari shi kuma yă sa wannan riga wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama, a kuma bi da shi a bisan doki ko’ina a titunan birni, ana shela a gabansa ana cewa, ‘Wannan shi ne abin da ake yin wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama!’ ”
10
Sarki ya umarci Haman ya ce, “Tafi yanzu ka karɓi rigar da dokin, ka kuma yi yadda ka shawarta wa Mordekai, mutumin Yahudan nan, wanda yake zama a bakin ƙofar sarki. Kada ka kāsa yin kome daga cikin abin da ka faɗa.”
11
Saboda haka, Haman ya karɓo rigar da dokin. Ya sa wa Mordekai rigar, ya kuma bi da shi a kan doki ko’ina a titunan birnin, yana shela a gabansa yana cewa, “Wannan shi ne abin da ake yi wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama!”
Settings