Skip to content
Esta 6:6-9

Esta 6:6-9

6
Sa’an nan Haman ya shigo, sai sarki ya ce masa, “Me ya kamata a yi wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama?” Haman dai ya yi tunani a ransa ya ce, “Wane ne sarki zai girmama in ba ni ba?”
7
Sai ya amsa wa sarki cewa, “Saboda mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama,
8
bari a kawo rigar sarautar da sarki ya taɓa sawa, da kuma dokin da sarki ya taɓa hawa, wanda aka sa kambin sarauta a kai.
9
Sa’an nan, bari a ba da rigar da kuma dokin wa ɗaya daga cikin manyan sarakuna mafi kirki na sarki. Bari shi kuma yă sa wannan riga wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama, a kuma bi da shi a bisan doki ko’ina a titunan birni, ana shela a gabansa ana cewa, ‘Wannan shi ne abin da ake yin wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama!’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options