Esta 2:9-15
9
Yarinyar ta gamshe shi, ta kuma sami tagomashinsa. Nan da nan ya tanada mata, ya ba ta man shafawa da abinci na musamman. Ya ba ta bayi mata bakwai da aka zaɓa daga fadar sarki. Ya kuma kai ta tare da bayinta zuwa wuri mafi kyau na gidan matan kulle.
10
Esta ba tă bayyana asalin al’ummarta da na iyalinta ba, domin Mordekai ya hana yin haka.
11
Kowace rana Mordekai yana kai da komowa kusa da harabar filin gidan matan kulle, domin ya san yadda Esta take, da kuma abin da yake faruwa da ita.
12
Kafin a kai kowace yarinya wurin Sarki Zerzes, sai ta gama watanni goma sha biyu cif ana yin mata kwalliyar da aka tsara, akan ɗauki watanni shida ana shafa mata man mur, a ɗauki watanni shida kuma ana shafa mata man ƙanshi da kayan shafe-shafe.
13
A kuma koya mata yadda za tă tafi wurin sarki. Aka ba ta duk abin da take so ta riƙe daga gidan matan kulle zuwa fadar sarki.
14
Da yamma za tă tafi can, da safe kuma ta dawo wani ɓangaren gidan matan kullen da yake a ƙarƙashin kulawar Sha’ashgaz, bābā na sarki, wanda yake lura da ƙwarƙwarai. Ba ta dawowa wurin sarki sai in ta gamshe shi, sai ya kuma kira ta da suna.
15
Sa’ad da lokaci ya yi da Esta (yarinyar da Mordekai ya ɗauka tamƙar ’yarsa, ’yar kawunsa Abihayil) za tă shiga wurin sarki, ba tă nemi a ba ta kome ba in ban da abin da Hegai, bābān sarki mai lura da gidan matan kulle, ya ba da shawara. Esta kuwa ta sami tagomashin kowa da ya ganta.
Settings