Esta 2:5-11
5
To, a cikin mazaunin masarauta a Shusha, akwai wani mutumin Yahuda, daga Kabilar Benyamin mai suna Mordekai, ɗan Yayir, ɗan Shimeyi, ɗan Kish,
6
wanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya ɗauka tare ’yan zaman bauta cikin waɗanda ya ɗauko daga Urushalima, tare da Yekoniya, sarkin Yahuda.
7
Mordekai yana da wata ’yar kawunsa mai suna Hadassa, wanda ya yi reno, ba ta da mahaifi ko mahaifiya. Ita ce yarinyar da aka santa da suna Esta. Kyakkyawa ce ƙwarai. Mordekai dai ya ɗauke ta tamƙar ’yarsa sa’ad da mahaifinta da mahaifiyarta suka mutu.
8
Da aka yi shelar umarni da dokar sarki, sai aka kawo ’yan mata masu yawa a mazaunin masarauta a Shusha, aka kuma sa su ƙarƙashin kulawar Hegai. Aka kawo Esta ma zuwa fadar sarki, aka danƙa ta wa Hegai, wanda yake lura da mata.
9
Yarinyar ta gamshe shi, ta kuma sami tagomashinsa. Nan da nan ya tanada mata, ya ba ta man shafawa da abinci na musamman. Ya ba ta bayi mata bakwai da aka zaɓa daga fadar sarki. Ya kuma kai ta tare da bayinta zuwa wuri mafi kyau na gidan matan kulle.
10
Esta ba tă bayyana asalin al’ummarta da na iyalinta ba, domin Mordekai ya hana yin haka.
11
Kowace rana Mordekai yana kai da komowa kusa da harabar filin gidan matan kulle, domin ya san yadda Esta take, da kuma abin da yake faruwa da ita.
Settings