Afisawa 6:4
Ana nuna aya 4 tare da mahallin da ke kewaye.
1
Ku ’ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan.
2
Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,
3
don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”
4
Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ’ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.
5
Ku bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya. Ku nuna musu halin bangirma, kuna kuma yin musu biyayya cikin dukan abu, da zuciya ɗaya kamar ga Kiristi kuke yi.
6
Ku yi aiki sosai, ba don kawai ku gamshe su sa’ad da suke kallonku ba. Da yake ku bayin Kiristi ne, ku aikata nufin Allah da dukan zuciyarku.
7
Ku yi aikinku da kyakkyawar niyya, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba mutane ba.
Settings